Wasu daga cikin gawarwakin mutanan da aka kashe a yayin wannan hari

A kalla mutum 45 sun mutu, galibinsu mata da kananan yarasakamakon wani harin rashin Imani da mutanen da ake kyautata zaton ‘yan kabilar Bachama ne suka kai rugagen Fulani a jihar Adamawa, majiyoyi da dama sun tabbatar da aukuwar wannan hari.

Harin dai ya faru, ‘yan lokuta kafin harin da aka kai wani Masallaci a karamar hukumar Mubi ta Arewa a safiyar ranar talata, inda aka kashe kimanin mutum 50 yayin da suke Salar Asubah.

Wadan da suka samu damar sulalewa sun ce, ‘yan kabilar Bachama ne suka kai harin, suna kuma rera wakokin yaki. Yayin da a ranar litinin da maraice suka kaddamar da wannan mummunan harin rashin Imani kan mata da yara kanana.

Harin dai an kaishi ne bayan almuru a yankunan fulani dake kauyikan Shafaran da Shawal da Gumara da Kima da Kadamti duk a yankin karamar hukumar Numan.

“Maharan sun isa kauyukan ne, a lokacin da galibin mazajen garin suka fita daga yankunan nasu, wasu sun tafi kasuwa, wasu kuma, sun je bikin aure a karamar hukumar Mayo-Belwa. Dan haka babu wanda ya san za’a kai wannan mummunan harin”.

“Ina kan hanya ta ta dawowa kauyenmu daga kasuwar Numan, na fara ganin bakin hayaki ya turnuke kauyenmu, mintoci kadan kuma, na hangi wasu gungun maharan ‘yan kabilar Bachama, sun kai kusan mutum 150 suna fitowa daga kauyen”

“Dan haka, dole tasa na gudu domin tsira da rayuwata. Amma dai sun yi mana muguwar barna, domin sun kashe mana mata da yara, sannan sun kone mana gidaje kurmus”

“Sun shigo kauyukan namu da miyagun makamai suna rera wakokin yaki cikin harshen Bachama suna dauke da Matsefata da majaujawa da adduna da bundigar gida ta mafarauta da sauran dangin muggan makamai”

“Dukkan wadan da suka jikkata a yayin wannan harin tare da gawarwakin mutanan da aka kashe, an kashe su zuwa babban asibitin garin Numan” Inji Oriwa Hammadu, daya daga cikin wadan da suka tserewa maharan.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Adamawan ta tabbatar da mutuwar mutum 30 akan wannan mummunan harin da aka kai rugagen Fulani.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Othman ABubakar, yace ana nan ana cigaba da gudanar da bincike domin kamo wadan da suka aiwatar da wannan mummunan harin rashin imani akan mata da yara.

Ana nan ana bincike ka’in da na’in domin ganin an cakumo duk wadan da suke da hannu a wannan mummunan harin rashin Imani.

A yayin da yake magana bayan kammala jana’izar wadan da suka rasu a yayin wannan harin rashin Imani, Shugaban kungiyar Miyatti Allah reshen Arewa maso gabas, Mafindi Danburam, yace, fiye da mutum 60 an tabbatar da bacewarsu ba’a gansu ba, yayin da muka ga gawarwakin mutane 45 da aka halaka.

Danburan yace, gawarwakin mutane 45 da aka samu, tuni aka sallace su, kuma aka yi musu jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar, a garin Numan.

“Muna kiran gwamnati cikin gaggawa ta aiwatar da bincike tare da gano wadan da suka kai wannan harin domin kauce daukar fansa.

“Dunburan yace, ba makawa wannan harin ‘yan kabilar Bachama ne suka kaishi, domin sun jima suna yiwa fulani baranar ssu bar garin ko sun dandana kudarsu.

“Kafin kai wannan harin, Mai garin Numan ya kirawo wani taro da sshugabannin fulani makiyaya dake garin, yana mai gargadinsu da su fice su bar garin, domin shirin aiwatar da wannan mummunan harin rashin Imani.

Mataimakin Gwamnan jihar Adamawa, Matins Babale, yayi kira ga al’ummar yankin da su zauna lafiya a yayin da ya kai ziyara yankin domin ganewa idanuna abinda ya auku.

Martins Babale, ya kuma yi Allah wadai da wadan da suka kai wannan hari na rashin imani, tare da shan alwashin kamo maharan domin su fuskanci shari’ah, sannan kuma yayi alkawarin yin adalci ga duk wadan da aka zalinta.

 

 

 

LEAVE A REPLY