Sridevi

Daga Hassan Y.A. Malik

Fitacciyar jarumar Bollywood Sridevi ta rasu a daren yau Asabar da misalan karfe 11:00 na dare sakamakon bugun zuciya da ya yi mata kwaf daya.

Sirikin jarumar, Sanjay Kapoor ya tabbatar da mutuwar Sridevi ta shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa jarumar ta mutu ne a Dubai, inda ta halarci bikin Mohit Marwah tare da mijinta da kuma karamar ‘yarta, Khushi.

Labarin mutuwar Sridevi ya girgiza masana’antar shirya finafinai ta Bollywood, inda tuni jarumai da dama suke ta bayyana alhininsu a shafinsu na Twitter.

Marigayiya Sridevi ta fara fitowa a finafinai a shirin finafinan yankin Tamil tun tana da shekaru 4 da haihuwa. Sridevi ta samu karbuwa a matsayin jaruma karamar yarinya inda nan-da-nan ta yi fice a matsayin jaruma karamar yarinya a finafinan Tamil, Telegu, Malayalam da Kannada.

Ta fara fitowa a finafinan Bollywood a shekarar 1975 a wani fim mai suna Julie, inda ta taka rawa a matsayin kanwar babbar jarumar fim din.

Sridevi ta fara fitowa a babban matsayi a shekarar 1978 a fim din Solva Sawan kuma tun faga lokacin likkafarta ta ci gaba da mikawa.

Finafinan Himmatwala, Mawali da Tohfa sune suka haskaka jarumar aka san ta a fadin duniyar finafinan Bollywood da masoya kallon finafinan Indiya.

Rawar da ta taka a wadancan finafinai da muka bayyana a sama sun sama mata gurbi a manyan finafinai kamar su: Sadma, Mr India, Chandni, Chaalbaaz, Nagina da kuma Lahme, finafinan da sune suka zamar da ita jaruma ajin farko.

Jaruma Sridevi ta dakata da fitowa a finafinai bayan da ta auri furodusa Boney Kapoor a shekarar 1996, sai dai marigayiya Sridevi ta dawo harkar finafinai a shekarar 2012 inda ta fito a matsayin babbar jarumar fim din English Vinglish, fim din da ya yi matukar nasara.

An karrama Sridevi da kanbin Padmashri a shekarar 2013 kuma a duk tsawon rayuwarta, ta karbi kanbuna har guda 5 na karmawa daga Filmfare awards.

LEAVE A REPLY