Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta gayyaci Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki domin bahasinsa kan harin fashi da makamai da akai kai a garin Offa na jihar Kwara.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar akalla mutane 22 ne suke garkame a hannun ‘yan sanda wadan da ake zargi da hannu cikin wannan harin fashi da makamai da aka kai a Offa a kwanakin baya.

A lokacin da aka kai wannan mummunan harinfashi da makami, akalla mutane 25 ne suka rasa rayyukansu ciki har da ‘yan sanda guda 9 da suke bakin aiki a lokacin.

Saidai wata majiya daga rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tsegunta mana cewar, biyar daga cikin mutanan da ake tsare da su, sun alakanta Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki da hannu wajen daurewa wanda suka kai harin gindi.

Haka kuma, Ayoade Akinnibosun wanda shi ne, jagoran ‘yan fashin, ya bayyana cewar su ‘yan bangar siyasar gidan Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne.

Ya kara da cewar, duk da cewar ba da umarnin Saraki suka kai harin Offa ba, amma dai shi (Saraki) shi ne yake daukar nauyinsu wajen gudanar da ayyukansu na ta’addanci.

Daga cikin abubuwan da ‘yan sanda suka kama a tare da mutanan har da wata mota da suka yi ikirarin Gwamnatin jihar Kwara ce ta basu ita.

LEAVE A REPLY