Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da wani ja game da kokarin da ‘yan sanda Nijeriya ke yi na kama shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bisa zarginsa da a ke yi da hannu a fashin bankin Offa da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

Shugaba Buhari ya karbi bakunci babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya zo don ya bashi rahoton yadda Saraki ke da hannu a fashin bankin da aka yi a Offa, jihar Kwara da wadanda ake zargi suka bayyana Sarakin a matsayin wanda ke samar musu da kayan aiki da kudade.

Majiyarmu ta bayyana yadda Ibrahim Idris ya shiga fadar gwamnatin tarayya da takardun shaida da suka tabbatar da hannun Sanata Saraki a wancan danyen aiki.

‘Yan sanda na dab da kama Sanata Bukola Saraki nan ba da dadewa ba sakamakon umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na cewa doka ta yi aikinta a kan ko ma wanene.

Hukumar ‘yan sanda ta gayyaci Saraki zuwa ofishinta na bincike da ke Abuja a jiya Lahadi don ya amsa tambayoyi kan fashin bankin Offa da ke jihar Kwara.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa, Jimoh Moshood ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya.

LEAVE A REPLY