Mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan harkoki majalisar dattawa, Ita Enang ya tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kasafin kudin shekarar 2018 da ‘yan majalisa suka mika masa bayan da suka amince da shi don ya zama doka.

Sai dai kuma, ‘yan majalisun sun yi karin Naira biliyan 508 a cikin ainihin kasafin kudin Naira tiriliyan 8.61 da Shugaban kasa ya gabatarwa da majalisun na tarayya a watan Nuwambar shekarar 2017 da ta shude.

Enang ya bayyana cewar fadar ta Shugaban kasa ta amshi kasafin kudin shekarar 2018 da ya kai Naira tiriliyan 9.12 wanda majalisun tarayya suka amince da shi domin ya zama doka, ya kuma bayyana cewar nan ba da jimawa ba zai gabatar da kasafin kudin ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

LEAVE A REPLY