Yusuf Buhari bayan da ya dawo daga jinya

Duk inda ka duba a fadar Shugaban kasa babu abinda kake ji sai ‘sam barka’ kowa na cikin murna da farinciki, Gwamnoni da Ministoci da manyana jami’an Gwamnati da dangi da abokai duk sun taru domin marabtar Yusuf Buhari da ya dawo daga jinya garau.

Idan baku manta ba, a ranar 26 ga watan Disambar 2017 DAILY NIGERIAN ta fara bayar da labarin wani mummunan hadarin babur da ya rutsa da Yusuf Buhari da abokinsa Bashir Gwandu yayin da suke wasan tseren babur.

Mai dakin Shugaban kasa, hajiya Aisha Buhari ta nuna murna da jin dadi da kuma yin godiya ta musamman ga ‘yan Najeriya bsa addu’o’insu ga danta Yusuuf Buhari wanda ya dawo garau bayan ya sha jinyar raunin da ya samua kasar jamus.

“Mun yiwa Allah godiya da ya dawo mana da namu Yusuf gida lafiya bayan da yaje jinya kasar waje”

“A madadin dukkan dangi da iyalan Shugaban kasa, muna mika matukar godiya a bisa addu’oin da aka dinga yi mana na samun saukin danmu bayan hatsarin da yayi”

“Allah ya saka muku da alheri, ya kuma shiryar damu baki daya zuwa hanya madaidaiciya” Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.

Yusuf Buhari ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Namdi Azikiwe dake Abuja a ranar Alhamis da daddare, tare da shi akwai ‘yar uwarsa Halima Buhari tare da rakiyar likitan mahaifiyarsa Aisha Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa ya tarbi Yusuf a fadar Gwamnati tare da Shugaban kasar akwai gwamnan jihar Kogi Yahya Bello sai Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau sai kuma karamin Ministan lafiya wanda shi ne ya taho da Yusuf Buhari tun daga filin jirgi.

LEAVE A REPLY