Alhaji Sule Lamido

Mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya caccaki tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido kan batun cin hanci da rashawa. Fadar Shugaban kasa ta ce, a jerin tattaunawar da tsohon Gwamnan kuma me neman tsayawa takarar Shugaban kasa yayi da ‘yan jaridu yana zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna wariya kan batun yaki da cin hanci a Najeriya.

Garbaa Shehu, yace, ‘yan Adawa masu irin wannan zargin a rude kawai suke shi yasa suke zargin Shugaba Muhammadu Buhari da nuna wariya kan batun yaki da cin hanci da rashawa, yace “Mutanan da suka tsiyata kasarnan, suka nannagawa ‘ya ‘yansu kudade a cikin asusun su na ajiya da dunkiyar kasa”.

“Ba komai ‘yan adawa suke yi ba, illa kokarin dakile kokarin kotuna da hukumar yaki da  yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati wato EFCC da sauran hukumomin Gwamnati da ke yaki da zambar kudade”

“A Najeriya ne kawai, shugaba zai kwashi kudin gwamnati wanda na jama’a ne, zai baiwa ‘ya ‘yansa dan kawai su yi wadaka son ransu, sannan daga baya ya zo yana babatu domin kare abubuwan da yayi na rashin gaskiya, yana karairayi akan kokarin Gwamnati na yaki da abinda suke yi na rashin gaskiya”

“Abu mafi muni ma sshi ne, irin wannan mutum, yana gaban shari’ah ana tuhumarsa da almundahana da dukiyar al’umma, amma shi ne zai dinga babatu wai ana yin rashin gaskiya, ko nuna wariya kan yaki da cin hanci da rashawa, wannan aishi ne dalilin da yasa wasu kasashe ke yiwa Najeriya dariya, wannan sam ba adawa bace abin da suke yi illa aikin jagaliya”

Kuma abinda mutane irin su SUle Lamido basu sani ba, irin Shari’un da ake yiwa ‘yan Adawa a kotuna, galibinsu an fara shariar ne tun zamanin Gwamnatinsu ta PDP tana kan karagar Mulki, balle su zargi wannan Gwamnati da nuna wariya ko bangaranci. A cewar Garba Shehu.

Me zaku ce kan wannan Martanida fadar Shugaban kasa ta yiwa Sule Lamido?

 

LEAVE A REPLY