Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed el-Rufai ya gindayawa Sanata Shehu Sani dan majalisardattawa mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisardattawan najeriya sharuddan sasantawa.

Sanata Shehu Sani dai na daya daga cikin Sanatocin da aka yanke tsammanin zasu tattara komatsansu zuwa jam’iyyar PDP mai adawa, daga cikin Sanatocin APC da ake ganin suna yunkurin ballewa.

Sanata Shehu Sani dai ya bayar da mamaki inda duk kuwa da sabanin da yake tsakaninsa da Gwamna el-Rufai ya amince ya cigaba da kasancewa a cikin jam’iyyar APC ba tare da yabi sauran takwarorinsa zuwa jam’iyyar PDP ba.

Shehu Sani yana daga cikin Sanatoci 42 da suka kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar nuna goyon baya da kuma jaddada mubaya’arsu ga Shugaba Buhari.

Da yake amsa tambayoyi a cikin wani shirin kai tsaye a gidan Radiyo ranar Alhamis, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana abinda Sanata Shehu Sani yayi da cewar ridda ce irin ta siyasa.

“Dole ne Shehu Sani ya gayawa al’ummar jihar Kaduna me yasa ya ci dunduniyarsu, ya yi amfani da matsayinsa wajen hana jihar Kaduna karbo bashin bankin duniya domin yin ayyukan da zasu taimaki al’umma.

 

LEAVE A REPLY