Bukola Saraki

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya bayyana cewar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da dukkan jagororin jam’iyyar APC na kasa sun amince cewar dole ne Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki ya aje mukminsa na Shugabancin majalisa tunda ya bar APC.

Oshiomhole ya bayyana ‘yan jaridar dake fadar Shugaban kasa haka ne, bayan da ya fito daga wata ganawa ta musamman da ya halarta ta sirri tare da Shugaban kasa a fadar Gwamnati dake Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari tare da Shugaban jam’iyyar APC na kasa na yin wannan ganawa ne yayin da jam’iyyar ta APC ta tsinci kanta a wani wadi na tsaka mai wuya, inda take fama da zurarewar jiga-jigan jam’iyyar a fadin tarayyar Najeriya.

 

 

LEAVE A REPLY