Daga Hassan Y.A. Malik

Mutum mafi arziki a fadin Afirka, Aliko Dangote, a jiya Alhamis ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya a gidansa da ke kan tsauni da ke garin Minna, babban birnin jihar Neja.

A tawagar da ta yi wa Dangote rakiya har da ‘yarsa Halima da mijinta Suleiman Bello da kuma wasu kusoshi na rukunin kamfanin Dangote.

Ganawar ta Dangote da Babangida ta shafe sama da awa guda ana yi, sai dai attajirin ya ki fadawa manema labarai dalilin ziyarar da kuma abubuwan da suka tattauna a zaman.

Mun gano cewa dai Dangote ya ziyarci Minna ne don ya raba kayan agaji na kimanin Naira miliyan 250 ga mata masu karamin karamin karfi guda 25,000 a karkashin gidauniyarsa ta Dangote Foundation.

Dangote ya samu rakiyar gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello da mataimakin masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Bala Ibn Na’Allah da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Neja, Mika’il Bmitosahi

LEAVE A REPLY