Hon. Bashir Baballe

Dan majalisar wakilai daga jihar Kano Bashir Baballe dan majalisa mai wakiltar Minjibir da Ungoggo a majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya, ya bayyanawa DAILY NIGERIAN dalilin da ya sanya Sugabannin majalisun biyu suka kira wani zama na gaggawa kuma na musamman a zauren majalisar wakilai.

Da farko dalilin kiran wannan zaman majalisar sam bai shafi tarayyar Najeriya ba, batu ne da ya shafi su Shugabannin Majalisun biyu, akan an janye musu jami’an da suke tsaronsu.

“ABin mamaki ne kwarai da gaske, ace lokacin da ake kashe al’ummar kasarnan a jihohi da dama, Shugabannin majalisun guda biyu ba su yi tunanin yin irin wannan zaman na hadaka ba, sai yanzu da bukatun kansu suka matso”

 

LEAVE A REPLY