Daliban makarantar Sakandiren Gwamnti dake garin Dapchi da aka sace, kuma aka dawo da su, sun isa birnin Maiduguri a ranar Lahadi akan hanyarsu ta komawa Damaturu bayan sun gama ganawa da Shugaba Buhari a Abuja.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar dalibai 104 daga cikin 110 da aka sace, wanda kuma aka sake su a ranar 21 ga watan Maris.

Daliban dai an kaisu birnin tarayya Abuja a wani jirgin soja, kuma suka isa Abuja da misalin karfe 10:00 na safe, wanda suka kunshi kwamandan soja dake Maiduguri.

Rahoton DAILY NIGERIAN ya bayyana cewar, daliban wadan da suka samu rakiyar manya manyan jami’an Gwamnati da kuma wakilan iyayan yara, sun bar garin Maiduguri a cikin jerin gwanonon motoci zuwa Damaturu,inda ake sa ran dankasu zuwa ga iyayansu.

Daya daga cikin iyayan yaran, Aliyu Maisambu ya bayyana jin dadinsa da wannan cigaba da aka samu.

NAN

LEAVE A REPLY