Hassan Y.A. Malik

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki, a jiya Asabar, a wajen taron zaben shugabannin jam’iyya a matakin jiha  da jam’iyyar ta gudanar a afadin kasa gabaki daya na jihar Kwara da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar, ya bayyana cewa a shirya ya ke da ya warwarewa ‘yan Nijeriya surkullen da ke cikin siyasa, domin ita siyasa ba abu ne da za a iya fahimtarta a dare daya ba.

Saraki ya ci gaba da cewa, “A yau idanun ‘yan Nijeriya ya koma kan siyasar jihar Kwara sakamakon abubuwa iri-iri da ke ci gaba da faruwa a kasar da ya shafi ‘yan siyasar jihar.

“Hakan na faruwa ne saboda babu wani abu da ya ke daidai a siyasa, shi yasa ma babu a inda za ka samu tsohon gwamna da wanda ya gaje shi da wanda ya gaji wanda ya gaje shi suna zama inuwa daya. Babu sai a wannan jihar.

“Za mu warwarewa ‘yan  Nijeriya sirrin da ke cikin siyasa da kuma yadda a ke taka rawar siyasa a kasar nan.

“Ina kira ga magoya baya da kar su damu da abubuwan da ke faruwa da mu a matakin siyasar kasar nan; daidai muke da abubuwan da a ke ƙuƙƙulawa, wuyanmu zai iya dauka.

 “In ku ka duba za ku ga annuri a fuskata, bani da damuwa domin na san magoya baya suna tare da ni a kodayaushe,” Saraki ya ce

LEAVE A REPLY