Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo

A bisa al’ada ta mafiya yawancin Ministocin tarayyar Najeriya, idan Shugaban kasa baya nan, kuma mataimakinsa zai jagoranci zaman majalisar zartarwa ta Shugaban kasa basu cika halarta ba ko da kuwa suna Abuja.

Sai dai a wannan makon abin ba haka yake ba, domin kuwa a kalla ministoci 28 ne suka halarci wannan zama na majalisar zartarwa ta fadar Shugaban kasa. Masu fashin baki na ganin cewar wannan baya rasa nasaba da matakin da Osinbajon ya dauka kan tsohon Shugaban hukumar tsaro ta DSS.

Wasu na ganin wannan na daga cikin dalilin da ya sanya Ministocin suka shiga taitayinsu, domin sun fuskanci halin mukaddashin Shugaban kasa na babu sani babbu sabo a harkar gudanar da aikinsa.

LEAVE A REPLY