Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta bayar da umarnin yin ‘yar tinke ko kato bayan kato wajen fitar da ‘Yan takarkaru a jihohin Adamawa da Zamfara da kuma Bauchi.

Tuni dai daman hankali ya tashi a jihar Zamfara dangane da yadda Gwamna Yari ya kakabawa al’ummar jihar Kwamishinan kudi na jihar Mukhtar Idris, inda suka bijirewa wannan zabi na Gwamna Yari.

’Yan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a jihar da suka kunshi Sanata Kabiru Marafa da Mamuda Aliyu Shinkafi da Ibrahim Wakkala sun hada kai wajen kalubalantar wannan zabin da Gwamna Yari yayi a jihar, inda suka ce sam ba zata sabu ba bindiga a ruwa.

Sai hakar ‘Yan takarar ta cimma ruwa domin kuwa uwar jam’iyyar APC ya kasa ta ce dole ayi kato bayan kato was wajen zaben fidda gwani.

Haka suma Gwamnonin jihohin Adamawa da Bauchi na cikin tsaka mai wuya, kasancewar da wuya su iya kai labari a zaben fidda gwani matukar za a yi kato bayan kato ko ‘yar tinke kamar yadda ake fada.

LEAVE A REPLY