Shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Tukur Yusuf Burtai

Daga Hassan Y.A. Malik

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar janar Tukur Yusuf Burutai, ya amince da yi wa sojoji guda 3,729 da ke karkashin Ofireshon  Lafiya Dole da ofireshon DEEP PUNCH II karin girma na musamman a sakamakon rawar da suka taka a yaki da Boko Haram a dajin Sambisa.

Kakakin rundunar sojin Nijeriyar, birgediya janar Texas Chukwu ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cewa karin girman ya yi la’akari ne da jarumtar sojojin a gumurzun da suke yi da Boko Haram.

Wadanda aka kara wa girman sun hada da nasu mukamin Staff Sergeant guda 223 da Sergeant guda 551 da Corporal guda 994 da Lance Corporal guda 1064 da kuma kurata guda 932.

Rundunar Ofireshon Lafiya Dole dai ita ke da alhakin fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram, inda a bisa wannan dalili ne aka kirkire ta.

LEAVE A REPLY