Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai yayin da yake kada kuri'arsa a mazabarsa dake unguuwar Sarki a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai yace ba damuwarsa bane ko wacce jam’iyya ce zata lashe zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kaduna ranar Asabar, Gwamnan yace abinda ya fi damunsa shi ne a yi gaskiya da adalci a yayin wannan zabe.

Gwamnan ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a mazabarsa dake unguwar Sarki a akwati mai lamba 024.

Yace Gwamnatinsa zata zama aain misali wajen gudanar da zaben kananan hukumomi na gaskiya a fadin tarayyar Najeriya.

 

LEAVE A REPLY