Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Talata zai tashi zuwa birnin Niamey na ƙasar Nijar domin halartan taron ƙasashen Afurka ta yamma, domin tattaunawa kan batun kudin bai daya da ƙungiyar ke shirin samarwa a yankin.

Taron da ake shirin farawa a ranar Talata zai samu halarta shugabannin ƙasashen ECOWAS don tattauna kan batun kuɗin bai ɗaya na yankin da ƙasashen Najeriya da Kwadebuwa da Ghana da Nijar suka nuna buƙatar samar da shi a yankin.

A yayin wannan taro, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi tare da Ministar kuɗi Kemi Adeosun da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Godwin Emeifele waɗan da zasu kasance tare da Shugaba Buhari a yayin wannan tattaunawa da sauran shugabannin kasashen yankin.

Ana sa ran, Shugaba Buhari zai dawo Abuja a ranar talatar bayan kammala taron na wuni guda. Wannan taro da Shugaba Buhari zai je Niamey yana zuwa ne, kwana daya bayan ya dawo daga wata ziyarar aiki da yaje kasar Turkiyya.

LEAVE A REPLY