Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Daga Yasir Ramadan Gwale

A wata wasika da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar dattawa a ranar talata, ya bukaci majalisar  domin ta sahale masa ya ciwo bashin dalar Amurka biliyan 5.5 daga kasashen ketate.

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ne ya bayyana hakan a zaman da majalisar tayi ranar talata, inda ya karantawa ‘yan majalisar wasikar da Shugaban kasa ya aiko musu domin neman amincewarsu a ciwo wannan bashi.

Shugaba Buhari dai ya bayyana cewar, za’a ciwo bashin ne domin tayar da komadar ayyukan da aka rattaba za’a yi su cikin kasafin kudin wannan shekarar ta 2017 mai karewa.

Shugaban Yace, bashin zai taimaka ne, wajen kamala ayyukan da aka faro, da kuma sauran wadan da suka rage ba’a yi ba, kuma an sanya su a cikin kasafin kudin wannan shekarar 2017.

Me ye ra’ayinku kan wannana bashi da Shugaban kasa yake son ciwo wa Najeriya. Shin ya dace a halin da ake ciki a karbowa Najeriya bashi?

LEAVE A REPLY