Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mince da nadin manyan daraktoci biyu na hukumar leken airi ta kasa NIA.

Mutanan da aka nada sune, Apollonius Agev, a matsayin jaka da musamman, sai kuma Kio Amieyeofori, wannan nadi kuma ya fara aiki nan take.

Idan ba’a amnata ba hukumar leken asiri ta kasa NIA ta auka cikin rudani biyo bayan nadin sabon Shugaban hukumar Rufai Abubakar, wanda aka ce bai cancanci wannan mukami ba saboda rashin kwarewa.

Sai dai kuma wannan nadi ya zo ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Talara, daga babban sakataren hukumar na dindidn ta ofishin Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya, Mista Olushegun Adekunle.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Apollonius Ageb daga jihar Binuwai (Arewa ta tsakiya) a matsayin jakada na musamman da kuma Kio Solomon Benibo Amieyeofori daga jihar Ribas (Kudu maso kudu) A matsayin mataimakin darakta a hukumar NIA.

 

LEAVE A REPLY