Shugaban Amurka Trump tare da Shugaba Buhari a fadar Gwamnatin Amurka dake White House a birnin Washington DC

Daga Hassan Y.A. Malik

Gawamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya bayyana bayanin da Sugaba Muhammadu Buhari ya fadawa Shugaba Donald Trump na Amurka game da fulani makiyaya na cewa wai basa yawo dauke da bindigun AK-47 sai sandunan korar shanunsu da kuma ‘yan addunan na saran rassan bishiyu don ciyar da garkensu a matsayin bayani na karya da son rai da kuma yaudara ga Trump din.

Gwamna Ishaku ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke zantawa da manema labarai jiya a Abuja, inda ya bayyana cewa lamarin ya sanya al’ummar jihohin Taraba dana Binuwai cikin wani yanayi na ji kamar mafarki suke ko gizo ne fulani makiyayan da suke gani dauke da bindigun AK-47 kuma suna yakar al’ummar jihohin tare da kashe su.

“Ba karamin kuskure bane Shugaba Buhari ya yi ikirarin cewa fulani makiyaya basa yawo dauke da bindigu. To in har basa yawo dauke da AK-47, waye ya ke kashe manoma a fadan makiyaya-da-manoma?”

“Maganr gaskiya ita ce, ya kamata mu fuskanci gaskiya da adalci wajen kawo karshen kashe-kashen da rikicin fulani makiyaya da manoma ke haifarwa a kullum kwanan duniya,” Gwamna Ishaku ya ce.

LEAVE A REPLY