GanawarShugaba Buhari da Sanatoci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC a daren jiya Laraba a fadar Gwamnati dake Aso Villa a Abuja. Sun yi ganawar ne ta sirri tsakanin Shugabannin jam’iyyarAPC da kuma Sanatocin na APC tare da Shugaban kasa.

Bayan fitowarsu daga wannan ganawa ne, Jagoran sanatocin Sanata Ahmed Lawan Yobe ya shaidawa manema labarai a fadar Shugaban kasa cewar, sun tattauna ne domin duba yuwuwar yadda zasu karbe ikon majalisar dattawa daga hannun Shugaban majalisar na yanzu Abubakar Bukola Saraki domin samun saukin aiwatar da ayyukan majalisar.

A cewarsa, yin wannan tattaunawa da kuma ganawa a yanzu ta zama dole, domin Shugaban kasa na gab da fara hutunsa na kwanaki goma, kamar yadda ya bayyana a rubuce cewar zai dauki hutun kwanaki goma.

Tuni dai Shugaba Buhari ya aikewa da majalisar dattawa da ta wakilai a rubuce cewar yana mai sanar da su cewar zai yi tafiya ta kwanaki goma a kasar burtaniya domin yin hutu, a saboda haka yake sanar musu cewar ya mika ragamar ayyuka a hannun mataimakinsa Yemi Osibanjo.

 

LEAVE A REPLY