Shugaba Buhari ya umarci Kiristoci su yi adduar bude taro har sau biyu a zaman majalisar zartarwa na yau laraba.

Ministan Ayyukan gona Audu Ogbe da Ministan kwadago Chris Ngige sune suka bude taro da adduah a zaman majalisar zartarwa na yau.

Bayan da SHugaban kasa ya umarci Audu Ogbe ya bude taro da adduah, ya sake kiran Ministan kasa na ma’aikatar Muhalli Jibril Ibrahim wanda bai samu halartar zaman ba. Daga nan Buhari ya kuma kiran Chris Ngige ya sake bude adduah a karo na biyu.

Chris Ngige ya shaidawa Buhari cewar shi fa Kirista ne, Buhari ya bashi umarnin yayi adduah kawai.

LEAVE A REPLY