Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamnan jihar Bunuwai Samuel Ortom

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamnan jihar Bunuwai Samuel Ortom suna yin wata ganawa ta musamman a fadar Gwamnati dake Ao Villa, Abuja.

Rahotanni sunce, Gwamnan ya isa fadar Gwamnati a Aso Villa dake Abuja da misalin karfe 10:05, inda kuma daga nan aka wuce da shi kai tsaye zuwa ofishin Shugaban kasa.

Wannan dai shi ne karon farko da Shugabannin biyu suke irin wannan ganawa tun bayan kashe kashen da aka yi a Jihar Bunuwai a makon da ya gabata, wanda ya tayar da kura a jihar.

A sabida haka wannan ganawa ta shugabannin biyu bata rasa nasaba da wannan batun kashe kashe. Kuma da alama anbatun ganin hanyoyin da za’a bi domin magance wannan rikici da ya auku a jihar.

Haka nan, a daren jiya aka jiyo fadar Shugaban kasa ta baiwa Sufeton ‘yan sanda na kasa umarnin ya koma Jihar Bunuwai har sai an samu dawowar doka da oda a yankunan da abin ya auku.

LEAVE A REPLY