Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani yayi kira ga matasan Najeriya da su yunkuro domin kwace ragamar ikon kasarnan daga hannun tsofaffin mutanen da basa iya tsinana musu komai.

Sanatan Yace kalaman Shugaba Muhammadu Buhari kan matasan wannan kasa abin takaici ne matuka. Shehu Sani yace, a lokacin da Shugaba Buhari yake jawabi a taron kasashen da kasar Burtaniya ta yiwa mulkin mallaka, Shugaba Buhari yaci fuskar matasan Najeriya, ta hanyar bayyana su a matsayin ‘yan zaman kashe wando.

A lokacin da yake maida martani kan kalaman na Shugaba Buhari a shafinnsa na Twitter, Sanata Shehu Sani, ya yi kira ga Shugaban da ya nemi afuwar matasan Najeriya, kan wadancan kalaman cin zarafi da yayi a garesu.

Ya bayyana cewar “Ya kamata Shugaban kasa ya janye wancan magana tasa, sannan ya nemi afuwar matasa, sannan ya saka musu da wani abu da zai sanya su farinciki a bisa halin damuwa da harzuka da suka yi”.

“Shugaban kasa mutum ne kamar kowa, zai iya yin kuskure, kuma masu magana sun ce, durkusawa wada ba gajiyawa bane, Shugaban kasa zai iya neman afuwar ‘yan Najeriya akan abinda yayi musu ba daidai ba”

“Haka kuma, yanzu ne lokacin da matasa zasu tashi domin kwace goruba daga hannun kuturu, su dawo da ikon kasarnan ya koma hannunsu domin cirewa al’ummar kasarnan suhe daga wuta” A cewar Sanata Shehu Sani.

 

LEAVE A REPLY