Mataimakin kakakin jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Timi Frank, ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya roki afuwar ‘yan Najeriya musamman matasa kan kalaman batancin da yayi garesu, inda ya bayyana matasan Najeriya da cewar malalata ne cima zaune.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, SHugaba Buhari, a yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Laraba gaban a Landan yace “Fiye da kaso 60 na ‘yan Najeriya matasa ne, wanda suke fama da jahilci basa yin aikin komai, suna jiran cin banza, saboda kawai sun dogara da cewar kasar tana da man fetur”

“Haka kuma, suna zaman banza ne, basa aikin komai, a haka kuma suke son samun gida da ilimi da kula da lafiyarsu duk kyauta”

A lokacin da take maida martani kan wannan kalami na Shugaba Buhari, karamin kakakin jam’iyyar APC na kasa, ya zargi Shugaba Buhari da cewar bai mutunta matasan najeriya ba, cin fuska ne a gaban kasashen duniya Shugaba Buhari ya bayyana haka”

Mista Frank, a cewarsa, fiye da matasa 20 ne suka rasa rayuwarsu, a shekarar 2014 a kokarinsu na neman aikin yi da za’a dauka a hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin rufawa kansu da iyalansu asiri.

Jigon APC din yace, Najeriya ce ke da fitattun mutane masu hazaka a duniya, yace Shugabannin Najeriya ne suka jefa al’umma cikin wannan mawuyacin hali.

“Idan da ace matasan Najeriya masu zaman kashe wando ne, da ba zaka same su duk inda ka shiga a duniya ba, suna neman na kansu. Muna da hazikan matasa da suke samar da ayyukan yi, ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba”

 

LEAVE A REPLY