Fatima Ganduje

Daga Hassan Y.A. Malik

Kano ta yi cikar kwari a yau da masu fada a ji daga bangarori daban-daban na kasar Nijeriya a wani yanayi shirye-shiryen daurin auren ‘yar gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da dan gwamnan Oyo, Idris Abiola Ajimobi da za a kulla a yau Asabar a masalacin Juma’a na jihar Kano da ke jikin fadar Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

Cikin mashahuran ‘yan Nijeriya da za su halarci taron har da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, gwamnonin jihohi akalla 20, ministoci da sauran masu rike da manyan mukaman gwamnati.

Tun a jiya Juma’a ne, mai dakin matamakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo tare da ‘yan rakiyar matan gwamnonin Nijeriya 15 suka sauka a Kano don fara halartar bukukuwan auren.

Tuni da fadar gwamnatin Kano ta sauya yanayi, inda aka kawata ta da ado da ke nuna al’adun Bahaushe da na Yarbawa, haka kuma a zafafa harkokin tsaro a fadin jihar don samar da tsaro ga mahalarta taron.

LEAVE A REPLY