Gwamnatin kasar Amurka ta baiwa Najeriya tallafin zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan 102 kimanin Naira biliyan 3.7, Gwamnatin ta kasar Amurka ta bayarda wannan makudan kudade ne domin tallafawa mutanan da suka tagayyara saboda rikicin Boko Haram da ya daidaita su.

Sashin dake kula da harkokin wajen kasar Amurka shi ne ya bayyana bayar  da wannan tallafi. Ya kara da cewar za’a yi amfani da wadannan kudade ne wajen samar da matsuguni ga mutanan da suka rasa gidajensu da kuma bayar da agajin kiwon lafiya da samar da abinci ga al’ummomin dake sansanonin ‘yan gudun hijira a Arewa maso gabas.

Ana kiyasta akalla mutane miliyan biyu ne wannan rikici na Boko Haram ya shafa kai tsaye ko a kaikaice. Kusan fiye da shekaru goma kenan mutanan da ke yankin Arewa maso gabas ko jihohin Borno da Yobe da Adamawa suke fama da wadannan tashe tashen hankulan da Boko Haram da wani reshe na kungiyar ISIS dake kudu da hamada Sahara suka jefa rayuwarsu a ciki.

Wadannan kudade zasu taimaka wajen samarwa da dubban mutane abinci da ruwan sha mai tsabta da mahalli da kula da lafiya bayar da agajin gaggawa ga wadannan damasifar Boko Haram ta raba su da muhallansu da guraren sana’o’insu da garuruwansu tare da jefa su cikin mawuyacin hali da matsananciyar rayuwar hannu baka hannu kwarya.

 

LEAVE A REPLY