‘Yan Najeriya ba wai kawai batun sayo kwancen motoci ne yake kai su birnin Kwatano na jamhuriyar Benin ba, sukan yo safarar karatun digiri na bogi a wasu jami’o’in da suma sunyi kama da na bogi.

Bayan da ‘yan Najeriya da dama suka koka, kan yadda wasu abokansu da ‘yan uwansu sukan je wannan kasa ta kwatano a jamhuriyar Benin domin samun digiri a kasa da lokacin da ya kamata a same shi, DAILY NIGERIAN ta tura wakilinta wannan kasa inda yayi bincike na musamman akan yadda batun yake.

Yanayin da ake samun digiri a wannan birni na Kwatano cike yake da ban mamaki kwarai, domin cikin ‘yan watanni dalibi kan samu shahadar kammala karatun digiri. Wannan ce ta sanya daliban da suka kasa cin jarabawa a Najeriya kan garzaya can domin samun garabasar digirin bogi.

DAILY NIGERIAN ta tattara bayanai inda ta gano cewar, jami’o’i da yawa a jamhuriyar Benin kan turo wakilai ko jami’ansu zuwa Najeriya, su shiga jami’o’i da kwalejoji da makarantu masu zaman kansu, domin tallata musu yadda zasu sami digiri cikin kankanin lokaci.

Wannan ta sanya ‘yan Najeriya masu kishi sukai ta nuna yatsa kan wannan sabuwar cuwa-cuwar samun digiri cikin kankanin lokaci. Ba tare da dalibai sun cika lokacin da ya kamata ace mai karatun digiri yayi ba, ake basu shahadar kammala karatun digiri din.

Wani karin abin mamaki dangane da faruwar hakan, shi ne yadda ‘yan dalibai ‘yan Najeriya da suka je irin wadannan jami’o’i kan tsallake zuwa yin hidimar kasa wato NYSC a Najeriya.

Binciken da wakilin DAILY NIGERIAN yayi ya gano cewar, Najeriya ita ce ke da mafiya yawan dalibai a wannan birnin na Kwatano a jamhuriyar Benin, suna samun digirori a fannoni daban daban a jami’o’in da mafiya yawancinsu ba halastattu bane.

Bincike ya nuna cewar akwai fiye da jami’o’i 100 masu zaman kansu a wannan kasar, amma jami’o’i guda biyu ne kacal na Gwamnati wanda suma suke fuskantar matsaloli kuma suke cikin mawuyacin hali.

Bincikenmu ya gano cewar, akalla akwai jami’o’i 40 da suka amince da amfani da Turancin Ingilishi a matsayin harshen da za’a a yi amfani da shi domin koyarwa a jami’o’insu, amma bai wuce guda 10 suka cika ka’idojin ma’aikatar ilimi ta jamhuriyar Benin ba.

Haka kuma, binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewar, mafiya yawancin wadannan jami’o’i ba su da kwararrun malamai da suke koyarwa, wasu malamai ne da suma galibi suke da takardun kammala karatu masucike da tuhuma suke koyarwa.

Wani dalibi dan Najeriya da yake karatu a wannan kasar, ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar,zance na gaskiya mafiya yawancin jami’o’in kasar harka kawai suke yi ta neman kudi, burinsu kawai shi ne waye ya zo da kudi su bashi digiri.

“Wasu jami’o’in a Kwatano suna baiwa dalibai damar samun gurbin karatu ba tare da la’akari da takardunsu da irin kwazonsu ba, kawai suna duba wanda ya zo da kudi ne, duk munin takardunsu matukarsuna da kudi zasu samu shahadar kammala digiri cikin sauki”

Wasu daga cikin jami’o’in da wakilinmu ya ziyarta sun hada da: Eco-Tes, ISFOP, King Amachree International School, ISM Adonai, Houdegebe North American University, Irgib Africa, Hill City University, the West African Union University, Iscom University, Esep Le berge University, Esgis University, Saint fecilite University, Les cour sonou da kuma ESAE University.

Bincikenmu ya tabbatar mana da cewar, wasu jami’o’inma suna aiki ne a gine ginen da suka kama hayarsu, ciki kuwa har da jami’o’in da suke ikirarin bayar da horo akan abubuwan da suka shafi kiwon lafiya.

Haka kuma, kwanannan, Hukumar ilimi ta jamhuriyar Benin ta bayar da sanarwar kin amincewa da dukkan wasu kwasa-kwasai da suka danganci kiwon lafiya a jami’o’i masu zaman kansu. Jami’o’in Houdegbe da Adonai ne kadai suka cika wannan sharadi na ma’aikatar ilimin kasar, yayin da sauran suke yi ta kazamar cuwa-cuwa.

Duk kuwa da cewar an soke iznin irin wadancan jami’o’i da basu cika sharudda ba, amma har yanzu akwai jami’o’i irinsu Eco-Tes da ISFOP da Hill City da kuma West African Uninion University da suke bayar da shahadar kammala karatu a matakan ilimin kiwon lafiya da dangoginsa, ba tare da suna da ko da dakunan gwaje gwajen kimiyya ba.

Duk da haka,akwai kwasa kwasai a wasu jami’o’in da ana karantar da su ba tare da wasu matsaloli ba,ma’ana babu yabo babu fallasa.

Wani daga cikin hukumomin jami’o’in da suka cika ka’ida, ya bayyana cewar “Zaku iya ganewa idanunku, tun daga yanayin gine ginen makarantun, kun san cewar mu kam da gaske muke yi anan. Haka kuma, idan kuka kalli malamanmu zaku ga kwararru ne, muna da dukkan abubuwan bukata, makaranta na da gidajen kwanan dalibai, mun baiwai dalibai ingataccen ilimi”

“Sabbin daliban da zasu yi digirin farko sukan yi shekara uku ne, yayin da daliban da zasu yi Difloma kan yi shekaru biyu suna daukar darussa daban daban kafin su kammala karatunsu a basu shahadar kammalawa”

Wani Farfesa mai suna James Rodrigue ya bayyana cewar tudadar ‘yan najeriya zuwa kasar domin neman karatun digiri ya bata al’amuran karatu a kasar.

Haka kuma, Farfesan ya bukaci hukumomi su yi abinda ya dace domin gyatta al’amura a harkar karatu a kasar.

“Wasu jami’o’in fa anan kasar, sukan yi sati biyar kawai a samista daya kuma su baiwa dalibai shaidar kammala karatun likitanci ko ilimin harhada magunguna ko injiniya ba tare da suna da ko da dakin gwaje gwajen kimiyya guda daya ba”

“Wasu jami’o’in kuma da aka hana musu koyar da darussan kimiyya sabida rashin cika kaidoji, zaka samu har yanzu suna bayarda darussa kan ilimin kimiyya da aikin lafiya a gine ginen da suka kama haya, ba tare da wani cikakken tsarin koyo da koyarwa ba”

“Akwai abin takaici kwarai da gaske, ace wasu dalibai kawai zasu biya kudi a basu shahadar kammala karatu ba tare da sun halarci ko da azujuwa domin daukar darasi ba”

Da yake bayar da misali akan irin halin da ake ciki, Musa habib, wani malami a jami’ar maryam Abacha dake jamhuriyar Nijar ya bayyana cewar akwai dalibin da aka kore shi sabida bai ci jarabawa ba, amma ya garzaya kwatano ya samu shahadar kammala digiri cikin wata daya.

“A yanzu haka yaron yana nan yana yin hidimar kasa wato NYSC” A cewarsa.

Dole ne anan a tuhumci Ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya,kan irin yadda take yadda da irin wannan gurbataccen digiri, har a baiwa masu shi damar yin hidimar kasa wato NYSC wannan kam abin takaici ne.

Wani dan Najeriya da yake zaune a birnin Kwatano, mai suna Aliyu Dikko, ya shaidawa wakilinmu cewar, ya sauya ra’ayinsa na kai yaransa makarantun kasar Benin sabida yadda yaga abin ya koma cuwa cuwa.

Ya kara da cewar “okacin da na kawo yarana guda uku nan domin su yi karatu, sun shaida min cewar zasu iya samun takardar kammala karatun digiri a cikin wata tara. Daga nan hankalina ya tashi na cika da mamaki, na sauya tunanin,inda naga gara na mayar da su najeriya su yi karatu a can”

Inda matsalolin suke:

Batun samun digiri a cikin kankanin lokaci a jamhuriyar Benin, yana daga cikin abinda aka fi tattauna shi a kafafen sada zumunta na intanet a najeriya. Wannan ya biyo bayan rubuce rubuce da akai ta yi akan irin yadda ‘yan najeriya ke zuwa suna yin cuwa cuwar digiri a wannan kasar.

Daga ina laifin yake? Ko shakka babu, hukumomin ilimi a jamhuriyar Benin suna da kaso mai yawa, sabida yadda suka kasa samar da tsari da kuma tabbatar da wanda ake da shi da ana tafiya akansa wajen baiwa dalibai ilimi a kasar.

Haka kuma, ofishin jakadancin najeriya dake jamhuriyar Benin, yana da rawar da zai taka sosai wajen baiwa dalibai ‘yan najeriya shawarar inda ya dace su yi karatu, da jami’o’in da ya dace su shiga.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun hukumar kula da jami’o’i ta Najeriya NUC, Ibrahim Usman Yakasai, ya bayyana cewar batun tunda yana da alaka da wata asa bai shafi NUC ba.

“Hurumin hukumar kula da jami’o’i ta NUC ya shafi iyaka Najeriya ne kadai. Kuma ba nine nake da hakkin yin magana kan wannan batu ba a yanzu, amma abinda zance shi ne, samun shahadar kammala digiri a cikin wata bakwai ko shekara daya wannan ba abu ne da hankali zai dauka ba, duk wanda ya samu irin wannan digirin yasan me ya samuwa kansa”

Haka kuma, mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta najeriya da kuma Jakadan najeriya a Jamhuriyar Benin duk sun kasa samuwa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY