Kwanaki hudu kacal bayan da sojin Nijeriyab suka fito kafafen yada labarai suka bayyana cewa sun yi nasara akan kungiyar Boko Haram kuma dajin Sambisa na hannunsu, sai ga shugaban kungiyar Boko Haram din, Abubakar Shekau ya fito a wani bidiyo da suka saki a jiya yana cewa har yanzu mayakan Boko Haram na nan a cikin dajin Sambisa tare da matan ‘yan sanda da suka sace suka yi garkuwa da su.

A makon da ya wuce ne dai kwamandan rundunar yaki ta Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya fito kafafen yada labarai ya yi ikirarin cewa sojojin Nijeriya sun ga bayan Boko Haram gaba daya da ke a dajin Sambisa tare kuma da cewa daruruwan ‘yan Boko Haram sun mika wuya ga sojin Nijeriya, haka kuma, sojojin sun ceto wasu daruruwan fararen hula da mayakan suka yi garkuwa da su.

 “Rundunata ta kutsa cikin kwaryar matsugunin Boko Haram da ake kira da Camp Zairo, kuma tuni sun karbe iko a dajin Sambisa. Mun fatattaki kungiyar Shekau tare da kauce maboyarsa. Yanzu haka sun tsere kuma muna binsu don mu karasa su.”

A wannan sabon bidiyo na Shekau da ya fita a jiya, Shekau ya karyata ikiririn sojin Nijeriya na cewa sun kore su daga dajin Sambisa, tare kuma da yin barazanar ci gaba da haddasa tashe-tashen hankula a fadin Nijeriya.

 Ga sabon bidiyon:

https://youtu.be/FeSZ2iYlm6U

LEAVE A REPLY