Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da ya kai ziyara kasuwarAzare da ta kone

A yayin ziyarar bazata da ya kaijihar Bauchi a ranar Alhamis da safe, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasuwar Azare da ta kone kurmus a makon nan.

Shugaban na ziyara a jihar Bauchi ne domin jajantawa al’ummar jihar bisa ibtila’in gobara da ya aukawa babbarkasuwar Azare dake yankin Katagum a jihar Bauchi.

Haka kuma, Shugaba Buhari na ziyara a jihar domin jajantawa al’ummar jihar bisa guguwa hade da iska mai karfin gaske da ta yi barna a sassan yankuna jihar baki daya.

Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar da mukarrabansa ne suka tarbi Shugaban kasa da ya sauka a jihar Bauchi da sanyin safiyar  wannan rana.

Bayan haka, Mai Martaba Sarkin Azare ne ya zagaya da tawagar Shugaban kasa da ta Gwamnan jihar Bauchi domin duba shaguna kimanin 700 da suka kone a cikin kasuwar ta Azare.

LEAVE A REPLY