Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana mamakinsa kan yadda yace “Ban san cewa Sifeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris bai tare a jihar Binuwai ba kamar yadda na bashi umarni sai ya” Shugaba Buhari yana bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da al’ummomin makiyaya da manoma a jihar Binuwai.

Shugaba Buhari ya bayyana mamakinsa da aka ce masa Sifeton ‘yan sanda na kasa ko awa 24 bai  yi ba a jihar Binuwai, alhali Shugaban ya bashi umarnin tarewa a jihar Binuwai har sai zaman lafiya ya dawo a dukkan fadin jihar tsakanin fulanimakiyaya da manoma.

“Bamu nade hannu muna kallo abubuwa suna faruwa haka sasakai ba, muna nan muna yin aiki tukuru wajen ganin mun kawo karshen wannan zub da jini da ake yi a jihar Binuwai dama dukkan sassan Najeriya da ake fama da tashin hankali”

“Ina kuma horonku da ku komawa aikin gona, musamman noman Shinkafa, domin na samu bayanin cewar an daina shigo da Shinkafa da kashi 90 zuwa Najeriya, sabida yadda wasu jihohi suka mayar da hankali kan noman Shinkafa, a sabida haka nake kiranku ku mayar da hankali kan naoman nan” A cewar Shugaba Muhammadu buhari.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Binuwai Samuel Orton, ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da a kara rubanya kokarin aikin soji a jihar domin samar da aminci da nutsuwa a tsakanin al’ummar jihar baki daya.

Sannan yayi kira ga al’ummar jihar Binuwai da su yi hakurin zama da juna lafiya, domin zaman lafiya yafi zama dan Sarki a cewar Ortom.

Gwamnan ya kuma bayyana cewar, samarwa da makiyaya burtali shi ne kadai mafitar dangane da rikicin da ake samu tsakaninsu da makiyaya, dan haka ya bukaci Gwamnatin tarayya da ta samarwa da fulani burtaloli domin yin kiwo.

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Miyatti-Allah reshen jihar Binuwai Malam Shettima Mohammed, ya bayyana cewar, sam ba adalci bane a zargi fulani da cewar sune suka yi wadannan kashe kashe a jihar Binuwai.

 

LEAVE A REPLY