Majalisar dattawa ta bukaci Ministar kudi, Kemi Adeosun da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN. Godwin Emefiele, da su gurfana gabanta saboda wata badakar fitar da kudi dala miliyan 462 domin sayan wani jirgi mai saukar ungulu.

Majalisar dai tace, ta samu bayanin an fitar da wannan zunzurutun kudi ga wani kamfanin kasar Amurka domin sayen jirgin helkwafta, haka kuma, a takardun sayen ance wai da sahalaewar majalisar kasa aka sayo jirgin, abinda majalisar tace ba tada masaniya.

A zaman majalisar dattawan na ranar Talata, Sanata Samuel Anyanwu (PDP Imo) ya mike domin ankararwa ga sashi na 80 karamin kashi na 1 da na 2 na kundin tsarin mulkin kasarnan na 1999.

Mista Anyanwu ya ce “Na samu tabbataccen labari cewara watan Maris 2018, an cire kudi daga asusun Gwamnatin tarayya, da yawansu yakai dala miliyan 462, aka biya domin sayen wani karamin jirgin helkwafta a kasar Amurka. Anyi wannan ne kuma ba tare da amincewar majalisar kasa ba.

“Na sani cewar, babu wata bukata da aka turo daga bangaren zartarwa domin sayen wannan jirgi zuwa gaban majalisar dattawa, daga asusun gwamnatin tarayya”

“A matsayina na dan majalisar dattawa ina bukatar majalisa ta yi bincike akan taya akai aka fitar da wadannan makudan kudade”

“Ina kuma fatan majalisa zata gayyaci Gwamnan Babban Bankin najeriya da Ministar kudi da ministan tsaro, domin su gaya mana yadda aka aka fitar da wadannan makudan kudade kuma aka biya wani kamfanin kasar Amurka, ba tare da sanin majalisar dattawa ko amincewarta ba”

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, wanda shi ne ya jagoranci zaman majalisar,  ya nemi ‘yan majalisar da su yi kuri’ah kan wannan batu ta hanyar amfani da muryarsu, kuma dukkansu suka amince da abinda takwaransu ya zo da shi.

Bayan haka kuma, mataimakin Shugaban majalisar ya mika alhakin wannan al’amari zuwa ga kwamitin kula da bin diddgi da ka’ida na majalisa da ya gayyaci mutanan da ake zargi kan wannan batu domin jin bahasi.

 

LEAVE A REPLY