Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnatin jihar kano tana kashe naira biliyan 110 duk shekara wajen biyan albashin ma’aikatan jihar kamar yadda kwamishinan yada labarai, matasa da al’adu na  jihar, Alhaji Ibrahim Garba ya bayyana.
Kwamishinan yace a kowanne wata gwamnatin jihar tana kashe naira biliyan 9.2 wajen biyan albashin ma’aikatan jihar su dubu dari da hamsin da daya.
Sannan yakara da cewa naira biliyan dari da goman da ake kashewa a duk wata na albashin ma’aikatan jihar banda albashin ma’aikatan kotu, dana ma’aikatan jami’o’in kimiyya da fasaha ta Wudil da kuma jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Ibrahim Garba yakara da cewa banda matsalar tattalin arziki dana haraji da ake fama dashi gwamnatin bata wasa wajen biyan ma’aikatan jihar albashi.
“Duk da cewa ana fama da matsalar tattalin arziki, babu wani ma’aikaci da yake bin gwamnati ko sisin kwabo, mun yarda cewa biyan albashi yazama dole saboda haka bama wasa da biyan ma’aikata hakkokinsu” inji Ibrahim Garba.
A karshe kwamishinan yace, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta dukufa domin ganin ta bunkasa ayyukan cigaba a jihar don walwalar al’umar jihar.

LEAVE A REPLY