A ranar Alhamis din nan, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai cigaba da jagorantar zaman majalisar zartarwa. Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaban kasa na musamman akan kafafan yada labarai ne ya sanar da hakan ranar laraba a Abuja.

Garba Shehu yace, Shugaban ƙasar zai cigaba da jagorantar zaman majalisar zartarwar ne a yau Alhamis domin tattauna wasu muhimman batutuwan da ya kamata a tattauna.  A zaman na jiya dai, majalisar ta amince a saki kudade domin gudanar da wasu manyan ayyukan raya kasa wadan da suka lamushe kudade kimanin Naira biliyan 300.

Haka kuma, Shugaban kasar a yayin zaman na jiya, ya rantsar da manyan sakatarorin Gwamnati guda shida acikin 22 da aka amince da su a farkon wannan shekara.

Wadan da aka rantsar din sun hada da: Mustapha Suleiman (Kano); Adekunle Adeyemi (Oyo); Comfort Ekaro (Rivers) Adebayo Akpata (Ekiti).

Sauran su ne, Dr Abdulkadir Muazu(Kaduna); Marcelinus Osuji (Imo) and Bitrus Nabasu (Plateau).

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN yace tuni mutum 15 daga cikin manyan sakatarorin suka sha rantsuwar kama aiki.

LEAVE A REPLY