Aiku Abubakar

Manya manyan ‘yan siyasar Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan kalaman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a Landan, inda ya bayyana matasan Najeriya da cewar cima zaune ne kuma jahilai.

A ranar Laraba a birnin Landan, Shugaba Buhari a yayin da yake gabatar da jawabi a taron zuba jari na kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka, yace da yawan ‘yan Najeriya ‘yan zaman banza ne, kuma jahilai, ba a shirye suke su yi aiki domin dogara da kansu ba, kawai sun dogara da cewar kasar tana da man fetur.

Tsohon  mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Ekiti Ayodele Fayose da kuma Sanata mai wakiltar jihar Bayelsa a majalisar dattawan Najeriya, Ben Bruce Murry sun caccaki Shugaba Buhari kan wannan kalami.

A cewar Atiku Abubakar, Matasan Najeriya masu hazaka ne, duk da wahalar da suke ciki suna yin kokari matuka domin neman na kansu, suna amfani da sabbin hanyoyi irinsu amfani da ilimin kimiyyar kwamfuta da nishadantarwa domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

“Na sha nanatawa cewar, man fetur ba shi ne kadai arzikin da Allah ya huwacewa Najeriya ba, matasanmu su ne babban arzikinmu a Najeriya, daga babu suka samar da Nollywood da kannywood wanda duk Afurka ake kallo kuma ake nishadantuwa”

Shima a nasa bangaren, Gwamnan jihar Ekiti Ayodele fayose, ya bayyana cewar matasan Najeriya jajirtattu ne, masu kaifin basira, duk da cewar tsofaffin mutane sun kanainaye komai na Shugabancin kasarnan, anki basu dama,amma duk da haka suna kirkiro abubuwa masu kyau domin cigabansu.

“Abin takaici ne kwarai da gaske, ace a karon farko tun 1999 a samu ‘yan daba sun shiga majalisa sun mamaye ta kuma har su ci nasarar sace sandar majalisar.

“Matasan Najeriya zakakurai ne, tsaffin mutane irinsu Buhari sune suka tare musu gaba wajen samun cigaba mai ma’ana, kuma ace wai za’a koma ana zagin matasa da cewar’yan zaman banza ne”

“Tsofaffin mutane irin su Buhari duk sun mamaye komai sune zasu yi, irin damar da suka samu a shekarun 50s da 60s sune kuma suka hana matasan yanzu samun irin wannan damar”

“Yana shekara 19 yabar Sakandire ya shiga aikin soja, yana da shekaru 21 ya zama Lutana kuma aka nada shi kwamandan yaki da ya jagoranci bataliya ta biyu a Abeokuta, me yasa matasan yanzu ba zasu samu irin wadannan damarmakin ba?”

Shima a nasa bangaren, Sanata Murray Ben-Bruce dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bayelsa a majalisar  dattawan Najeriya, ya bayyana cewar, duk wanda ya kira matasan Najeriya da cewar cima zaune ne, to da alama baya iya bambance dama da hauni.

LEAVE A REPLY