Atiku Abubakar

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta bayyana matsayarta kan ficewar Alhaji Atiku Abubakar daga jam’iyyar. Jam’iyyar ta ce, Atiku Abubakar dan siyasa ne da sam sam ba shi da alkbila.

A ranar juma’a ne dai tsohoaimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki, abinda bai yiwa wasu ‘yan jam’iyyar dadi ba.

Dubban magoya bayan jam’iPDP ne dai suka karbi tsohon mataimakin shugaban kasar a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Yola a ranar Asabar da ya je jiharsa ta Adamawa domin shiryeryen komawarsa jam’iyyar PDP.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar dai, ya wuce ta’aziya ne bayan saukarsa a Adamawa inda dubban magoya bayansa suka raka shi gidan wani aminisa da ya rasu domin yin ta’aziya ga iyalansa.

A lokacin da yake maida martani kan wannan batu, jami’in tsare tsare na jam’iyyar APC ta jihar Adamawa, AhmedLawan ya bayyana cewar jam’iyyar sam bata damu da ficewar Atikun daga jam’iyyar ba, ya ce ficewarsa bata tayar musu da hankali ba.

“Bamu taba daukar tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da wani muhimmanci ba, domin mun san shi din dan siyasa ne marar alkibla, kuma mai tsalle tsalle. Kuma ficewar tasa ba zata kawowa jam’iyyar wata gagarumar matsala ba kamar yadda ake zato.

“Jam’iyyar APC, jam’iyya ce ta dukkan al’ummar Najeriya ba wasu ‘yan tsiraru ba. Kuma talakawan da suke cikin jam’iyyar APC sune abin alfaharinmu.”

LEAVE A REPLY