A ranar talatar nan ne, tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyarar mubayi’a Sakatariyar jam’iyyar PDP ta ƙasa dake babban birnin tarayya Abuja. Atiku Abubakar ya isa harabar Sakatariyar PDP ne bisa rakiyar daruruwan magoya bayansa.

Shugaban kwamatin riƙo na jam’iyyar Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ne ya tarbe shi yayin da ya isa Sakatariyar PDP din. Atiku ya bayyana cewar, PDP daman gidansa ne da aka gina tare da shi, kuma yanzu hali ne yasa dole ya yiwa PDP kome.

Ya bayyana cewar, ya dawo ne domin taimakawa a sake farfado da martabar jam’iyyar tare da taimakawa wajen ganin PDP ta samu nasara fiye da wadda ta samu a baya. Atiku Abubakar dai ya raraka kirarin jam’iyyar PDP tare da fatan samun nasararta.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin riƙo na jam’iyyar Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya bayyana jin dadinsu da dawowa gidan da Atiku Abubakar yayi, Makarfi ya bayyana Atiku Abubakar da cewar haziƙi ne kuma jarumi.

Sai dai daga bisanian kulle kofa  tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da Ahmed Makarfi, inda suke yin wata ganawar sirri. Idan ba’amanta ba, a kwanaki biyu da suka gabata ne, Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP bayan da ya fice daga APC.

LEAVE A REPLY