Kasar Amurka ta bayyana rufe ofishin jakadancinta dake babban birnin tarayya Abuja na da wani lokaci. Wannan ya fito ne a wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar a shafina na intanet a yau da safe.

A saboda haka dukkan wasu harkokin da ake gudanarwa a ofishin jakadancin dake Abuja zasu koma Legas, haka nan kuma, dukkan wadan da suka tura bukatun neman iznin shiga kasar Amurka, suma ana umartar su da su tuntubi ofishin jakadancin dake Legas.

Ana kuma kiran Amurkawa dake zaune a Arewacin najeriya, da su tuntubi ofishin jakadancin Amurka dake Legas idan akwai wata bukatar gaggawa da suke da ita.

Babu dai wata cikakkiyar sanarwa da ta bayyanarda dalilin rufe ofishin jakadancin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 

LEAVE A REPLY