Shugaban Amurka Trump tare da Shugaba Buhari a fadar Gwamnatin Amurka dake White House a birnin Washington DC

Daga Hassan Y.A. Malik

A ci gaba da ziyarar aiki da Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ke yi a kasar Amurka, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi gargadi ga takwaransa na Nijeriya cewa, kasar Amurka ba za ta lamunci kisan ‘yan addinin Kirista da ke dada yawaita a Nijeriya ba.

“Kashe-kashen ‘yan addinin Kirista da ke kara yawaita ba karamar matsala bace. Za mu yi aiki ba dare ba rana don ganin mun kawo karshen wannan matsalar domin kasar Amurka ba za ta lamunci ci gaba da faruwar kashe-kashe ba.”

Shugaba Buhari ya yi alkawarin yin aiki ka’in da na’in wajen ganin gwamnatinsa ta kawo karshen matsalar kashe=kashe musamman a arewa maso yammacin Nijeriya.

Ya kuma yabawa gwamantin Amurka bisa amincewa da ta yi na sayarwa da Nijeriya jiragen yaki don yakar ta’addanci.

LEAVE A REPLY