Marigayi Mustapha Akanbi

Allah ya yiwa tsohon Babban Alkalin kotun daukaka kara Mai Shari’ah Mustapha Akanbi rasuwa.

Akanbi shi ne mutumin da ya kirkiro hukumar hukunta masu cin hanci da rashawa ta kasa ICPC dama sauran hukumomin Gwamnati da dama dake batun yaki da cin hanci da rashawa.

Iyalansa sun bayyana cewar ya rasu da misalin karfe 2 na safiya, ana sa ran kuma za’a yi jana’izarsa yau Lahadi kamar yadda yazo a cikin koyarwar addinin Musulunci.

An haifi marigayi Mustapha Akanbi a shekarar 1932 a birnin Akara na kasar Ghana, sannan yayi karatunsa ne a Najeriya da kuma kasar Burtaniya.

Mustapha Akanbi ya kafa kamfanin Lauya a kano, sannan yayi aiki a gurare da dama a ma’aikatar Shariah ta kasa.

Yayi riyata bayan ya shafe shekatu 25 yana aiki a gurare daban daban, daga bisani kuma tsohon Shugaban kasa Obasannjo ya nada shi a matsayin Shugaban hukumar ICPC na farko.

Marigayin yana da lambar girmamawa mafi daraja ta kasa GCFR.

LEAVE A REPLY