Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar Allah shi ne zai hukunta tsaffin Shugabannin kasarnan musamman Jonathan da Obasanjo akan yadda suka yi barnar da suka yi da dukiyar da Allah ya huwacewa Najeriya ita.

“Yan Najeriya shaida ne cewar, babu tituna a kasar, babu hanyar jirgin kasa, babu hasken wutar lantarki duk kuwa da abinda ake cewa an kashe miliyoyin daloli domin samar da su ga al’umma bau komai da zaka iya gani, Allah shi ne kadai zai hukunta wadannan mutane” A cewar Shugaba Buhari.

Ya kara da cewar, lokacin da ya shiga ofis, ya bukaci Gwamnan babban bankin Najeriya da ya bashi bayanin kudaden da suke asusun Gwamnatin tarayya, amma sai yaji abinda ya bashi mamaki tare da tayar asa da hankali, inda aka tabbatar masa da cewar babu komai a asusun Gwamnatin tarayya.

“A zamanin shekaru 16 na mulkin PDP Najeriya na samun zunzurutun kudi kusan dala miliyan 2.1 sau 100 a kullumta hanyar cinikin manfetur, amma sai ka yi mamaki kusan an wawashe kudin baki daya, babu wani abu da zaka nuna wanda PDP ta yiwa Najeriya a wannan shekaru 16 da ta yi” Inji Shugaba Buhari.

 

 

LEAVE A REPLY