Shugaban hukumarzabe ta kasa, farfesa Mahmud Yakubu

Shugaban hukumar zabe ta Kasa mai Zaman kanta INEC, Farfesa Mahmoud Yakub ya bayyana cewar yadda yake ganin faya fayen bidiyo da ‘yan siyasa ke barazanar zubar da jini dangane da zaben 2019 ya sashi tunanin yuwuwar rage zaben.

Irin bidiyo da ke nuna za a zubda jini da ake yadawa a sabbin kafafen sadarwa na zamani, akwai ban tsoro yadda ‘Yan Siyasa ke nuna ko a mutu ko ayi rai dangane da zaben 2019. A cewar Shugaban hukumar zabe ta Kasa.

Yace dokar da ta kafa hukumar ta bashi iznin dagewa ko dakatar da zabe matukar idan ya fahimci za a yi amfani da zaben wajen Tatar da hankalin al’umma.

Shugaban hukumar na wannan bayani ne ga turawan zaben na jihohin kasarnan a lokacin da yake jawabi don shirin zaben Gwamnan jihar Osun da za ai a cikin wata me kamawa.

LEAVE A REPLY