Sanata Godswill Akpabio

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa na jam’iyyar PDP Sanata Godswill Akpaabio tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom na iya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a kwanne lokaci daga yanzu a cewar wata majiya mai karfi daga jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta APC ce dai ta fara zawarcin Akpabio a lokacin da ake ta sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Ko a makon da ya gabata jam’iyyar PDP ta shirya wata liyafar cin abinci ga wadan da suka tsallako daga jam’iyyar APC zuwa PDP din, amma ba’a ga Sanata Akpabio ba a wajen taron, abinda yake kara nuna cewar yana shirin komawa APC ne.

LEAVE A REPLY