Shugaba Muhammadu Buhari

Ya zuwa yanzu rahotanni na cewar adadin mutanan da aka kashe a harin rashin Imani da aka kai a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa ya kai mutum 60.

Shugaban kungiyar Miyatta Allah ta kasa reshen jihar Arewa maso yamma, ya tabbatarwa da DAILY NIGERIAN cewar adadin wadan da suka rasu a wannan mummunan harin rashin Imani ya kai mutum 60, sabanin alkaluman da aka bayar na mutum 45 a jiya.

Sai dai har ya zuwa wannan lokaci, fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari bata ce komai ba akan abinda ya faru a garin na Numan, masu magana da yawun fadar Shugaban kasa, Femi Adeshina da Garba Shehu babu wanda yayi magana a madadin Shugaban kasa kan wannan batu.

LEAVE A REPLY