Jagoran 'yan Shiah na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky

Jagoran ‘yan Shiah na Najeriya, Sheikh Ibrahim Yakub el-Zakzaky ya tattauna da manema labarai yau da rana.

PRNigeria na daga cikin ‘yan jaridun da suka ci nasarar tattaunawa da Zakzaky, kuma sun tattauna da shi ta minti daya da dakika 20, a yayin da Malamin yake amsa tambayoyin manema labarai a inda ake tsare da shi a birnin tarayya Abuja.

A lokacin Sheikh Zakzakya na sanya da farar babbar riga da farin rawani irin wanda ya saba sanyawa, inda kai tsaye ya nufi inda ‘yan jarida suke tsaye suna jiransa, daman an shirya hakan tuntuni.

‘Yanjaridu kuma suka dakace shi, inda suka je gab da shi da abin daukar magana, sunyi masa tambayoyi kuma ya amsa.

‘Yan jarida: Barkan ka da yamma, yallabai?

Sheikh Zakzaky: Yaya kuke?

‘Yan jarida: Zamu iya tattaunawa da kai?

Sheikh El-Zakzaky:  Eh, zaku iya tattaunawa da nni idan, idan mutanan sun bari.

‘Yan jarida: Yaya kake a halin da kake ciki?

Sheik El-Zakzaky: Ina nan cikin koshin lafiya, masu lura da ni (Jami’an tsaro) suna bani damaina ganawa da likitana, kuma Ina godiya ga Allah,ina samun sauki sosai.

‘Yan jarida: Shin kana da wani abu da zaka kara cewa bayan wannan?

Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya da addu’o’inku.

‘Yan jarida: Muna godiya yallabai.

 

LEAVE A REPLY