Shugaba Buhari yayin da yake ganawa da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara

Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Bukola Saraki tare da kakakin majalisarwakilai ta tarayya Yakubu Dogara a ranar Larabaa suka yi wata tattaunawa ta musamman tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan batun da ya shafi tsaro da matsalolin da kasarnan ke fuskanta.

Ofishin kakakin majalisar wakilai ta tarayya dake babban birnin tarayya Abuja, ya fitar da wata sanarwa cewar Shugabannin majalisun dokokin guda biyu su ne suka nemi a yi wannan zaman tare da Shugaban kasa domin tattauna matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

“A wannan rana, ni da Shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki, muka gana tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan rikicin da ya faru a jihar Filato”

“Mu ne muka nemi a yi wannan ganawa domin tattauna irin matsalolin da suka dabaibaye wannan kasar da suka shafi tsaro, domin duba hanyoyin da za’a kawo karshen kashe kashen da ake yi na babu gaira babu dalili a Najeriya”

“Haka kuma, mun yi amfani da wannan damar muka baiwa Shugaban kasa shawara akan matakan da ya dace ya dauka wadan da zasu samar da dawwamammen zaman lafiya mai dorewa a Najeriya”

“Bayan haka kuma, mun yi kira ga dukkan hukumomin da suke da alaka da bayarda agajin gaggawa ga wadan da suke cikin bala’i da su taimakawa wadan da wannan masifa ta shafa da aubuwan bukata na gaggawa”

 

LEAVE A REPLY