Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Lahadi ya bayyana dalilin da suka sanya shi kaucewa halartar babban taron jam’iyyar APC na kasa da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Idan baku mance ba, DAILY NIGERIAN ta habarto muku cewar tsohon Gwamnan ya kaucewa halartar babban taron jam’iyyar na kasa a Abuja, inda  maimakon hakan ya kaiwa tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wata ziyara ta musamman inda kuma daga bisani suka yi wata ganawa a kebe su biyu.

Wata sanarwa da PRNigeria ta samu, tsohon Gwamnan ya bayyana cewar “Yaki halartar taron ne domin kaucewa jin kunya, da kuma abubuwan da zasu kawo yamutsi da kuma hautsini a wajen babban taron jam’iyyar”

“Saidai duk da haka, kungiyarda nake jagoranta ta Kwankwasiyya a jihar Kano tana taya sabon zababben Shugaban jam’iyyar na kasa Kwamared Adams Oshiomhole da dukkan sabin zababbun Shugabannin jam’iyyar da aka zaba a mataki na kasa murna samun wannan mukami da suka yi, muna kuma yi musu fatan alheri” A cewar Sanata Kwankwaso.

LEAVE A REPLY