ABIN ƁOYE: Gwamnatin Taraba cikin sirri ta baiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar...

ABIN ƁOYE: Gwamnatin Taraba cikin sirri ta baiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar umarnin sakin wadan da suka kashe Fulani 800

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

A wata wasikar sirri da DAILY NIGERIAN ta samu, an jiyo Gwamnatin jihar Taraba ta hannun Antoni janar na jihar kuma Kwamishinan Shariah Yusuf Nya Akirikwen na baiwa Kwamishinan ‘yan sandan jihar umarnin ya saki mutanan da ake zargi da kisan Fulani 800 a tsaunin Mambila dake yankin karamar hukumar Sardauna jihar Taraba.

Rikicin baya bayan nan da ya barke a jihar Taraba a ranar 17 ga watan Yunin 2017, tsakanin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai da kuma Fulani makiyaya, yayi sanadiyar asarar rayuka da kuma dumbin dukiyoyi masu yawan gaske.

Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu, wanda yake daya ne daga cikin shugabannin kwamitin amintattun kungiyar Fulani ta Miyatti Allah, ya bayyana cewar akalla Fulani 800 aka kashe a wata tattaunawa da aka yi da shi a baya bayan nan, a sanadiyar wannan rikici da ya barke a jihar ta Taraba.

“A wani kisan rashin imani, wata mace da cikinta aka halaka ta, aka farke cikinta, aka ciro abinda ke cikinta shima aka yanka shi. Ni da kaina na gabatarwa da Gwamnatin tarayya dukkan bayanai da kuma shaidun da suke nuna irin wannan rashin imani da aka yiwa Fulani aka kashe mutane kusan 800, har da sunaye da unguwannin mutanan da aka kashe na gabatarwa da gwamnatin tarayya”

“Babu wani mataki da aka dauka tun bayan da na mika wancan bayani. Ina kuma da tabbacin hukumomin sun kalli bidiyon irin kisan rashin imani da akayi, da kuma muryoyin da suke nuna hannu manyan ‘yan siyasar jihar Taraba. Babu ko mutum guda da aka kama balle a hukunta shi, an kashe Fulani a Numa da Kajuru” A cewar Sarkin Kano.

Amma a wasikar da aka aikewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, wadda aka rubuta a ranar 8 ga watan Satumbar, 2017, Mista Akirikwen yaki aiwatar da abinda ya dace akan mutanan da ake da tabbacin sune suka aikata irin wannan mummunan kisan gilla.

“A wasu rahotanni ko bayanai da suka zo ofishina, a baya bayan nan, sun nuna cewar, abinda ya farubiyo bayan harin tsaunukan Mambila a yankin karamar hukumar  Sardauna, wanda rikicin ya barke tsakanin 17 zuwa 20 ga watan Yunin 2017, an kama tare da garkame da yawan mutanen d ake zargi sun aikata wannan danyan aikin kisan rashin imani, wanda ofishinka ne ya aiwatar da wannan kame kamen mutanen” A cewar wasikar.

A cewarsa, tunda yake an kafa kwamitin sauraren bahasin wannan rikici, kuma ana bayar da bayanan yadda lamarin ya auku, to yin irin wancan kame kamen mutane na babu garira babu dalili bai dace ba, tunda an riga an kafa kwamitin bincike da sauraren bahasi.

“Mun samu labarin cewar, bayan da aka riga aka kaddamar da kwamitin saurare da bincike da kuma bibiyar bahasi, rundunar ‘yan sanda karkashin ikonka, ta dinga kame mutane babu gaira babu dalili tana garkame su, ko da kuwa me mutanan da aka kama din suka aikata, kamen bai dace ba, tunda akwai kwamitin bincike da gwamnati ta assasa, wannan abinda kayi ba komai yake nunawa sai tsabar kaucewa hanyar aikinka, ka koma yin bita da kulli, wanda kwamitin da Gwamnati ta kafa shi ne yake da hakkin yin wancan abu da rundunarku take yi” A cewar wasikar da kwamishinan Shariah na Taraba ya aikewa da Kwamishinan ‘yan sandan jihar.

Haka kuma, ya bayyana cewar, lokacikadan kafin barkewar wannan rikici, Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti mai kama da wannan,  domin tsare barkewar rikici da karyewar doka da oda a yankin a sanidar sabanin da ake samu dangane da mallakar filaye a yankin.

A sabida haka,Antini janar kuma Kwamishinan Shari’ah na jihar ya baiwa kwamishinan ‘yan sanda umarnin sakin dukkan mutanan da hukumarsa ke tsare da su da sunan wancan rikici, a kuma ajje dukkan wani zargi ko tuhume tuhume da ake yi musu kan wancan batu.

“Idan kuwa aka yi la’akari da wannan yanayin na neman samun zaman lafiya da fahimtar juna, wannan shawara ce ta kashinkaina, cewar dukkan mutanan da aka kama kuma ake zarginsu dangane da wannan rikici a gaggauta sakinsu ba tare da wani bata lokaci ba, sannan a ajje dukkan wasu tuhume tuhume da ake yi musu kan wannan batu” A cewar wasikar.

A sakamakon wancan rikici da ya auku a watan Yuni na shekarar 2017 da ta gabata, bayan sun tabbatar da cewar akalla Fulani 17,000 suka tsre daga yankunan domin neman tsira.

Daga cikin rugagen Fulanin da wannan rikici ya shafa sun hada da Nguroje, da na tsaunukan Mambila da Babagasa da Donadda da Katibu da kuma Megoge.

A lokacin da DAILY NIGERIAN ta tuntubi Attoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ah na jihar Taraba, yaki yadda ya karyata ko gasgata wannan wasika, inda ya nemi a tura masa da kwafi na wannan wasikar kafin yace wani abu akai.

Ko a lokacin da wakilinmu ya karantawa Kwamishinan wani sashi daga cikin wannan wasikar, Mista Akirikwen ya sake bukatar lallai sai an tura masa kwafin wasikar ya gani da idonsa kafin ya yadda yace wani abu game da wasikar.

Bayan haka, kwamishinan yaki yadda ya bayar da akwatin imel din da za’a aika masa da wannan wasikar, domin aike masa da kwafi kamar yadda ya nema tun farko.

LEAVE A REPLY

%d bloggers like this: