Wata kungiyar ‘yaan ta’adda a yankin Mambila suna cigaba da kaiwa Fulani munanan hare hare a rugagensu dake yankin dake Tsaunin Mambila, a yankin karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta samu tabbacin cewar akalla an kashe mutane 20, yayin da aka kashewa Fulani sama da shanu 300 a cigaba da hare haren da akae kai musu a yankin.

Wani magidanci Saadu Mogoggo da ya tsere daga inda lamarin ke aukuwa, ya bayyana cewar gidansa dake yankin Lemu a Gembu an kai musu mummunan hari, kuma tuni biyu daga cikin ‘yan uwansa suka rigamu gidan gaskiya, kuma dukkan shanunsu an karkashe su a yammacin Asabar din da ta gabata.

“A halin da ake ciki, yanzu haka bamu iya binne gawarwakin ‘yan uwanmu da aka kashe ba. Wannan kisa na kabilanci da ake kaiwa yankunanmu a Leme, an kashe mana mahaifi a watan da ya wuce. A yayin wannan harin an kwashe mana sama da shanu 100 an tafi da su har yau sai labarain”.

“Yan uwana guda biyu, sun sanarwa da wasu sojoji dake aikin kiyaye zaman lafiya a yankin namu, domin taimaka musu dawo da shanun da aka sace mana amma shiru kake ji”

“Abin takaici, akan haka, dan uwana yana kokarin bibiyar hakkinmu aka kashe shi, sojoji suna ji suna gani ana kai masa hari amma suka gudu”

Haka kuma, wani magidancin mai suna Abdu Gagarau, ya bayyana cewar “Kone kone da kashe kashen da ake yi suna ta karuwa kamar wutar daji har a safiyar yau. Suna kai mana hare hare tun ranar alhamis, fiye da mutane 20 ne suka mutu a yayin wannan hari da aka kai mana”

A lokacin da aka tuntube shi, dan majalisa mai wakiltar Nguroje da Gembu a majalisar dokokin jihar, Bashir Muhammad ya tabbatar da wannan abin takaici dake faruwa a yankin. An yi shiru ana kashe fulani babu ji babu gani a Tsaunin Mambila.

 

 

Abin takaici ne kwarai yadda wannan abin takaici yake cigaba da faruwa ana kallo an ki daukar mataki da gangan. Ana kai wadannan hare haren tun ranar Alhamis har zuwa ranar Lahadi amma babu wani mataki da aka dauka alhali mutane na ta mutuwa tare da halaka musu shanu.

Wani bincike ya nuna cewar an fara wannan rikici tun ranar Alhamis akan rikicin mallakar wani fili tsakanin Fulani da kuma kabilar Mambila a kauyen Yerimeru, daga nan rikicin ya warwatsu zuwa wasu sassan yankunan dake da makotaka.

LEAVE A REPLY